Take a fresh look at your lifestyle.

Kwankwaso ya musanta zargin sauya sheka da gwamnan Kano zai yi zuwa APC

19

Wata sanarwa da mai taimaka wa Kwankwaso kan harkokin yada labarai Saifullahi Hassan ya fitar ta bayyana rahoton da wani dandali na yanar gizo ya wallafa a matsayin karya da yaudara kuma ba tare da wani dalili na gaskiya ba.

 

Hassan ya ce Sanata Kwankwaso ya tsaya tsayin daka kan akidu hangen nesa da kuma manufofin jam’iyyar NNPP yana mai jaddada cewa an zabi Gwamna Yusuf ne a kan tsarin jam’iyyar kuma ya kasance mamba mai nauyin da ya rataya a wuyanshi na tabbatar da aikin da al’ummar Jihar Kano suka ba shi.

 

Sanarwar ta kuma kara da cewa Sanata Kwankwaso bai amince ko kuma nuna goyon bayansa ga duk wani yunkuri da ake zargin gwamnan ya yi na sauya sheka zuwa jam’iyyar APC ba inda ta kara da cewa ikirari da wasu ke yi na yin kuskure ne da gangan.

 

Ta kuma bukaci jama’a da magoya bayan jam’iyyar da kuma kafafen yada labarai da su yi watsi da rahoton da su dogara kawai da tabbatattun majiyoyi masu inganci don samun ingantattun bayanai.

Comments are closed.