Kotun daukaka kara a Mauritaniya ta yanke wa tsohon shugaban kasar Mohamed Ould Abdel Aziz hukuncin daurin shekaru 15 a gidan yari tare da ci tarar dala miliyan 3 lamarin da ya kara dagula hukuncin cin hanci da rashawa a shekarar 2023.
Tsohon Janar din soja ne wanda ya hau mulki ta hanyar juyin mulki sau biyu kafin ya zama shugaban kasa daga 2009 zuwa 2019 inda aka same shi da laifin karkatar da kudade da kuma wadatar kansa ta haramtacciyar hanya.
Masu binciken sun ce ya tara kadarori sama da dala miliyan 70 a cikin shekaru goma da ya yi yana mulki. Ya ci gaba da zama a gidan yari tun lokacin da aka yanke masa hukunci a shekarar da ta gabata.
Shari’ar dai ta ja hankalin duniya a matsayin wani misali da ba kasafai ake samun wani shugaban kasa a Afirka da ake zargi da cin hanci da rashawa a lokacin da yake kan karagar mulki ba.
Tawagar lauyoyin Aziz ta yi watsi da tuhumar da ake yi da alaka da siyasa inda ta yi zargin cewa sun samo asali ne daga sabani da magajinsa shugaba Mohamed Ould Cheikh Ghazouani.
A shekarar 2020 kwamitin majalisar ya kaddamar da bincike mai zurfi kan zargin cin hanci da rashawa a lokacin gwamnatinsa inda a karshe ya kama wasu 11.
Hukuncin na ranar Laraba da ta gabata ya wanke wasu manyan jami’ai shida daga tsohuwar gwamnatin Aziz amma ya amince da hukuncin daurin shekaru biyu a gidan yari kan surukinsa bisa zargin yin sari.
Kotun ta kuma ba da umarnin rusa gidauniyar “Errahma” (Mercy) da Dan Aziz ke gudanarwa tare da ba da izinin kwace kadarorinsa.
Hukuncin Aziz na iya zama wani muhimmin a tarihin siyasa da shari’a na Mauritania wanda ke nuna wani mataki mai karfi na yaki da cin hanci da rashawa a tsakanin manyan jami’ai.
Duk da haka lamarin ya ci gaba da dagula al’amuran siyasa a kasar da cibiyoyin ke ci gaba da karfafa ka’idojin demokradiyya.
Africanews/Aisha.Yahaya, Lagos