Firayim Ministan Habasha Abiy Ahmed ya bukaci kasashen Afirka da su hada kai wajen bunkasa fasahar kere-kere na gida (AI) don ciyar da manufofin ci gaban nahiyar.
Abiy ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi a wani babban taro mai taken AI da aka gudanar a ranar Asabar da ta gabata a Addis Ababa babban birnin kasar Habasha mai taken: “Yi amfani da AI don ci gaban Afirka da hadin gwiwa.”
Firayim ministan ya ce nahiyar Afirka na shiga wani yanayi mai sauyi a tsarin ci gabanta AI na gida zai iya zama mai samar da wadata mai amfani ta hanyar shigar da wani muhimmin ci gaba a cikin nasarar shirin raya nahiyar Afirka na shekaru 50 ajandar 2063.
“A yau mun tsaya a kan wani sabon zamani wanda ke da alƙawarin samar da wadata ga nahiyarmu wanda ke haifar da sababbin abubuwa a cikin AI kuma yana da damar hanzarta aiwatar da ajandar Tarayyar Afirka 2063 ” in ji Abiy.
Ya jaddada bukatar Afirka ta tsara AI bisa ka’idojinta yana mai cewa Habasha na zuba jari a fannin samar da ababen more rayuwa da fasahohi masu alaka da AI kuma tana kokarin fassara hangen nesanta zuwa wani tasiri mai inganci.
Xinhua/Aisha.Yahaya, Lagos