Take a fresh look at your lifestyle.

Shugaba Tinubu Ya Gana Da Alaafin Oyo Oba Oyooade

442

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya karbi bakuncin Alaafin Oyo na 46 Mai Martaba Sarkin Oyo Oba Abimbola Akeem Owoade a fadar gwamnati dake Abuja.

Ganawar shugaban kasa da Alaafin na Oyo na gudana ne jim kadan bayan da shugaba Tinubu ya kammala wata ganawar sirri da shugabannin tsaro da kuma mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Mallam Nuhu Ribadu.

Rahotanni sun bayyana cewa gabanin ziyararsa ta farko ga shugaban kasar rahotanni sun bayyana cewa Oba Oyooade ya isa Abuja babban birnin kasar ne a ranar Larabar da ta gabata domin gudanar da wata ganawar sirri da shugaban kasa kuma babban kwamandan tarayyar Najeriya Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

Tawagar shugaban kasa tare da sarkin gargajiya sun nuna mahimmancin cibiyoyi na gargajiya a harkokin mulkin Najeriya da kuma ci gaba da hadin gwiwa tsakanin gwamnatin tarayya da sarakunan gargajiya.

Shugaba Tinubu a lokacin nadin sarautar Oba Owooade a watan Afrilun 2025 ya bukaci sabon Alaafin da ya samar da hadin kan al’ummar Yarabawa da kasa baki daya.

Aisha.Yahaya, Lagos

Comments are closed.