Take a fresh look at your lifestyle.

Shugaban kasa Tinubu Ya Isa Birnin Rome Domin Bikin Rantsar Da Paparoma Leo Na 14.

35

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya isa Rome babban birnin kasar Italiya domin halartar bikin rantsar da Paparoma Leo na 14.

Shugaba Tinubu ya isa filin tashi da saukar jiragen sama na soja na Mario De Bernardo da ke birnin Rome da misalin karfe 1800 na safiyar ranar Asabar domin halartar wani gagarumin taron Fafaroma Leo XIV Bishop na Rome na 267 kuma sabon shugaban Cocin Roman Katolika.

Shugaban kasa Najeriya ya samu tarba daga manyan jami’an gwamnatin Najeriya.

Wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta fitar tun farko ta bayyana cewa ziyarar ta shugaba Tinubu zuwa birnin Rome zuwa ne bisa gayyatar da fadar Vatican ta yi masa biyo bayan zaben Fafaroma Leo na 14 da Majalisar Cardinal ta yi.

A cewar fadar shugaban kasa wata wasika da Cardinal Pietro Parolin ya aike wa Shugaba Tinubu ta nuna jin dadin da Paparoma ya yi da kasancewar shugaban Najeriya ya bayyana hakan a matsayin muhimmiyar “a wannan lokaci mai matukar muhimmanci ga Cocin Katolika da kuma duniya da ke fama da tashe-tashen hankula da rikice-rikice.”

Paparoma Leo ya ci gaba da nanata cewa “Al’ummarku mai girma ta fi soyuwa a gare ni yayin da na yi aiki a ofishin Apostolic Nunciature a Legas a cikin shekarun 1980.”

Tawagar ta Shugaba Tinubu sun hada da Karamin Ministan Harkokin Waje Ambasada Bianca Odumegwu-Ojukwu da Archbishop na Owerri da Shugaban taron Bishop-Bishop Katolika na Najeriya da Archbishop Lucius Ugorji da Archbishop Ignatius Kaigama na Abuja da Alfred Martins na Legas.

Aisha.Yahaya, Lagos

Comments are closed.