Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta ce jam’iyyun siyasa 16 sun shigar da fom din tsayawa takara a zaben gwamnan Jihar Anambra da misalin karfe 6:00 na yamma a ranar Litinin 12 ga watan Mayun 2025 lokacin da aka rufe tashar da aka kebe kai tsaye.
Wamishinan yada labarai da wayar da kan masu zabe na kasa Sam Olumekun a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai ya ce jam’iyyun siyasa 16 sun cika sharuddan da doka ta tanada.
Ya ce “Kamar yadda aka tanada a sashe na 29 (3) na dokar zabe ta 2022 kuma an jera shi a matsayin sashi na 4 na jadawalin lokaci da jadawalin ayyukan zaben hukumar ta buga bayanan kowane Dan takara da abokin takararsa ta hanyar nuna kwafin form EC9 tare da dukkan ma’aikatun da suka biyo baya a ofishinmu na kananan hukumomi 2 da ofishinmu na karamar hukumar Anambra.
Ya ce hukumar tana kira ga ‘yan Najeriya da su binciki takardun.
“Duk wani mai neman tsayawa takara da ya halarci zaben fidda gwani na jam’iyyarsa tare da dalilai masu ma’ana don ganin cewa bayanan da Dan takara ya bayar na karya ne zai iya kalubalantar zaben a babbar kotun tarayya kamar yadda sashe na 29 (5) na dokar zabe ta 2022 ya tanada.”
Ya kara da cewa za a fitar da jerin sunayen ‘yan takara na karshe a ranar 9 ga watan Yuni 2025 wato akalla kwanaki 150 gabanin ranar zabe daidai da tanadin sashe na 32(1) na dokar zabe ta 2022 da kuma jera shi a matsayin abu na 7 a jadawalin da ayyukan zaben.
An shirya gudanar da zaben gwamnan Jihar Anambra a ranar Asabar 8 ga watan Nuwamba 2025.
Yayin da zaben ya rage saura watanni 6 INEC na taka tsantsan na bin sharuddan doka don tabbatar da zabe.
Aisha.Yahaya, Lagos