Take a fresh look at your lifestyle.

Gwamnatin Najeriya Ta Yaba Da Rawar Da Kamaru Ke Takawa Wajen Tabbatar Da zaman Lafiya A Yankin

38

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta yaba da himma da hadin gwiwar kasar Kamaru wajen samar da zaman lafiya a yammacin Afirka a cikin mawuyacin hali na barazanar tsaro da kungiyar Boko Haram da sauran kungiyoyi masu dauke da makamai ke yi a yayin bikin cika shekaru 53 da samun ‘yancin kai.

Ministan Harkokin Waje Amb. Yusuf Tuggar a cikin wata sanarwa da kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Kimiebi Ebienfa ya fitar a Abuja ya taya takwaransa Lejeune Mbella ministan harkokin wajen Kamaru murna.

 

Yayin da kasar Kamaru ke bikin wannan gagarumin ci gaba Najeriya ta sake jaddada aniyarta da zurfafa dankon zumunci da hadin gwiwa tsakanin kasashenmu biyu.

“Har ila yau muna sa ran ci gaba da yin hadin gwiwa a cikin tsare-tsaren kungiyar Tarayyar Afirka (AU) da sauran tsare-tsare na bangarori daban-daban na duniya don ciyar da muriyar jama’armu da ma nahiyar baki daya.

“Najeriya na ci gaba da tsayawa tsayin daka wajen tallafawa kokarin Kamaru na inganta hadin kai da zaman lafiya da ci gaba mai dorewa,” in ji Tuggar.

Ministan ya yi fatan Allah ya ba gwamnati da al’ummar kasar Kamaru murnar zagayowar ranar samun ‘yancin kai da kuma karin shekaru masu yawa na ci gaba da zaman lafiya.

 

 

NAN/Aisha . Yahaya, Lagos

Comments are closed.