Ma’aikatar Kudi a Uganda ta sanar da rattaba hannu kan yarjejeniyar bayar da kudade dala miliyan 800 da bankin raya Musulunci.
Kudaden dai za su tallafawa ayyukan raya kasa da dama da suka hada da shirin shimfida layin dogo na hanyar jirgen kasa da nufin bunkasa harkokin kasuwanci da ababen more rayuwa a kasar.
Wannan yunƙurin na da nufin haɓaka kasuwanci da haɗin kai ga ƙasar gabashin Afirka da ba ta da teku.
Hanyar dogo za ta hade da makwabciyarta Kenya Standard Gauge Railway da kuma zuwa tashar ruwan tekun Indiya ta Mombasa.
Sauran ayyukan da za a samar da su a karkashin yarjejeniyar shekaru uku za su kasance a fannonin kiwon lafiya da sufuri da samar da makamashi.
Ramathan Ggoobi babban jami’in fasaha na ma’aikatar kudi da mataimakin shugaban bankin Rami Ahmed ne suka sanya hannu kan yarjejeniyar a taron shekara-shekara na bankin raya kasa da hedkwatar Saudi Arabiya a Algiers in ji ma’aikatar a X ranar Laraba din da ta gabata.
Reuters/Aisha.Yahaya, Lagos