Take a fresh look at your lifestyle.

Shugaba Tinubu Ya Taya Ayo Obe Murnar Cika Shekaru 70

21

Shugaba Bola Tinubu ya taya fitacciyar ‘yar gwagwarmayar dimokradiyya kuma lauya Mrs. Ayo Obe murnar cika shekaru 70 da haihuwa.

Fadar shugaban kasa a cikin wata sanarwa da ya mika sakon yabon shugaba Tinubu ga mai shari’a kan yadda take nuna kishin kasa da halayen da suka bayyana rayuwarta na hidima da gwagwarmayar samar da al’umma mai adalci da inganci.

“Rayuwar ku na jajircewa da kwazon a cikin hidima wanda aka misalta da tsawon shekarun na gwagwarmaya da rashin adalci da cin zarafin bil’adama har zuwa lokacin a matsayi ‘yar kasa masu ra’ayi iri daya don kalubalantar mulkin kama-karya na soja a cikin duhun ranakun al’umma ko da a cikin kasadar kare lafiyar  da ’yancin ku abin yabawa sosai.

“Ina alfahari da irin gudunmawar da kuka bayar wajen dora mulkin dimokuradiyya kuma a yau mun himmatu wajen bunkasar ta da kuma karfafa ta ” in ji Shugaba Tinubu.

Ayo Obe mai fafutukar kare hakkin bil’adama a lokuta daban-daban ya kasance shugaban kungiyar ‘yancin jama’a (CLO) kungiyar sa ido kan canjin yanayi a Najeriya memban hukumar ‘yan sanda da kuma tsakanin 2006-2009 ya jagoranci shirin zabe na Democratic Institute Abuja.

Shugaban ya yi addu’ar Allah ya ci gaba da baiwa mai kishin kasa lafiya ta yadda za a ci gaba da yi wa kasa hidima a hanyar fafutukar da take yi na samar da al’umma da kuma bil’adama Zaman Lafiya.

 

Aisha. Yahaya, Lagos

 

 

Comments are closed.