Take a fresh look at your lifestyle.

Uganda Na Hasashen Kashi 15% Na Samar Da Kofi.

23

 

Uganda na shirin samar da kofi a cikin shekarar noman 2025/26 (Oktoba-Satumba) inda zai karu da kashi 14.8% daga lokacin da ya gabata, wanda aka samu ta hanyar amfanin gona daga sabbin gonakin da aka shuka, in ji wani babban jami’i daga ma’aikatar aikin gona a ranar Alhamis da ta gabata

Kasar gabashin Afirka ita ce kan gaba wajen fitar da wake a nahiyar kuma galibi tana noma nau’in Robusta.

Yawan samarwa da fitar da kayayyaki yana karuwa sosai a cikin ‘yan watannin nan, yana hawa farashin kofi a duniya da karin girbi daga sabbin bishiyoyi.

A cikin shekarar noman da ta kai watanni 12 zuwa watan Satumba mai zuwa, Uganda na fatan samar da buhunan kofi mai nauyin kilogiram 60 miliyan 9.3, sabanin hasashen da aka yi na buhu miliyan 8.1 a shekarun baya, in ji Gerald Kyalo, kwamishinan sashen kofi a ma’aikatar aikin gona.

“Babban dalili shi ne karuwar shuka, manoma da yawa sun shuka kofi, wanda muke tsammanin zai fara noma a wannan shekara kuma ba makawa zai kara kaimi ga fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje,” in ji shi.

A tsawon shekaru, gwamnatin shugaba Yoweri Museveni ya yi ta raban irin shukar kyauta ga sabbin da tsofofin manoma domin fadada gonakinsu ko bude sabbin filayen noma.

Haka kuma gwamnati na taimakawa manoma da taki kyauta domin ganin kasar ta cimma burinta na samar da buhu miliyan 30 a duk shekara nan da shekarar 2030.

A cikin watanni 12 zuwa watan Agusta, Uganda ta samu dala biliyan 2.2 da fitar da kofi da take fitarwa, wanda ya karu da kashi 57% daga lokacin da ta gabata, a cewar bayanai daga ma’aikatar.

 

 

Aisha. Yahaya, Lagos

Comments are closed.