Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bukaci sabbin shugabannin ma’aikata da aka nada da su zurfafa kwarewa, taka tsan-tsan, da hadin kai a cikin rundunar soji yayin da suke yi wa kasa hidima cikin daraja da kwazo.
Shugaban ya bayar da wannan umarni ne a wata sanarwa da aka fitar a shafin sa na X, @officialABAT, yayin da yake sanar da sauye-sauye a tsarin shugabancin tsaron kasar.
Ya ce sabbin nade-naden na daga cikin kokarin da ake yi na karfafa gine-ginen tsaron kasa da kuma inganta ayyukan aiki.
“Na amince da sauye-sauye a cikin manyan jami’an sojojin mu don kara karfafa tsarin tsaron kasa na Najeriya.
Ina kira ga sabbin shugabannin ma’aikata da su zurfafa kwarewa, taka tsantsan, da hadin kai a cikin rundunar sojojin mu yayin da suke yi wa al’ummarmu hidima da daraja.”
A sabon tsarin, tsohon babban hafsan soji, Laftanar Janar Olufemi Oluyede, ya zama babban hafsan tsaro; Manjo-Janar Waheed Shaibu shi ne babban hafsan soji; An nada Air Vice Marshal Sunday Kelvin Aneke shugaban hafsan sojin sama; shi kuma Rear Admiral I. Abbas an nada shi babban hafsan sojojin ruwa.
Manjo-Janar Emmanuel Akomaye Parker Undiendeye ya ci gaba da rike mukaminsa na shugaban hukumar leken asiri ta tsaro.
Shugaba Tinubu ya kuma nuna godiya ga shugaban hafsan tsaron kasar mai barin gado, Janar Christopher Musa, da sauran tsaffin hafsoshin tsaro saboda “bautar da kai da kuma jajircewarsu,” yana mai tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa sabbin nade-naden da aka yi na nuna aniyar gwamnatinsa na tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali a Najeriya.
Aisha. Yahaya, Lagos