Take a fresh look at your lifestyle.

Vietnam Ta Nada Sabbin Mataimakan Firayim Minista Guda Biyu

22

Majalisar dokokin Vietnam ta tabbatar da nadin sabbin mataimakan firaminista biyu da ministoci uku.

Mataimakin firaministan ya kuma hada da tsohon ministan harkokin cikin gida Pham Thi Thanh Tra da tsohon shugaban jam’iyyar gurguzu na lardin Gia Lai Ho Quoc Dung.

Kara karantawa: Vietnam ta yi bikin samun ‘yancin kai na 80 tare da Parade na Tarihi

Majalisar ta kuma tabbatar a ranar Asabar din da ta gabata na nadin ministocin harkokin waje, noma da na cikin gida. Majalisar ta fara zamanta na karshe na bana a ranar Litinin, wanda za a kammala ranar 11 ga watan Disamba.

Wannan zaman dai na gabanin taron shekara biyar na jam’iyyar gurguzu ta Vietnam a cikin watan Janairu wanda zai ayyana manyan tsare-tsare da manufofin kasar nan da shekaru biyar masu zuwa sannan kuma ana sa ran za a zabo sabuwar tawagar shugabanni.

 

REUTERS/Aisha.Yahaya, Lagos

Comments are closed.