Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya gana da sabbin shugabannin ma’aikata da aka nada a fadar gwamnati da ke Abuja, a ci gaba da kokarin karfafa gine-ginen tsaron Najeriya.
Shugabannin ma’aikatan sun halarci zaman sirri ne biyo bayan nadin da aka yi musu kwanan nan, wanda fadar shugaban kasar ta bayyana a matsayin wani shiri na inganta kwarewa, da sabunta kwarjini a cikin rundunar soji.
Wadanda suka halarci taron da shugaban kasar sun hada da babban hafsan hafsoshin tsaro, Janar Olufemi Oluyede; Babban Hafsan Sojin kasa, Manjo Janar Waheedi Shaibu; hafsan hafsoshin sojin sama Air Vice Marshall Kennedy Aneke, da Rear Admiral Idi Abbas, babban hafsan sojin ruwa.
Har yanzu dai ba a bayyana cikakken bayani kan tuhume-tuhumen da shugaban kasar ya yi wa sabbin shugabannin sojojin ba.
Aisha. Yahaya, Lagos