An dawo da zirga-zirgar jiragen sama kai tsaye tsakanin Indiya da China, lamarin da ke nuna ci gaban dangantakar kasashen biyu sannu a hankali.
A ranar Litinin Da ta gabata ne jirgin IndiGo mai lamba 6E 1703 daga Kolkata ya sauka a Guangzhou, dauke da fasinjoji kusan 180.
An dakatar da zirga-zirgar jiragen sama tsakanin kasashen biyu a farkon shekarar 2020 saboda annobar COVID-19 da tashe-tashen hankula bayan wani kazamin fada da ya barke a yankin iyakar Himalayan da ake takaddama a kai.
Dakatarwar ta dauki sama da shekaru biyar, wanda ya shafi tafiye-tafiye, yawon bude ido, da musayar kasuwanci.
Ana sa ran sake dawo da aiyukkan zai saukaka tuntubar jama’a, da inganta harkokin kasuwanci, da tallafawa daidaita mu’amalar kasashen biyu sannu a hankali, a cewar gwamnatin Indiya.
Fasinjoji sun yi maraba da ci gaban, tare da lura da cewa “Jirgin sama na kai tsaye zai rage lokacin tafiya da sauƙaƙe kasuwanci da tafiye-tafiye na sirri.”
Krishna Goyal, wani fasinja mai tafiya kasuwanci, ya ce; “Jirgin saman za su karfafa kasuwanci da alakar kasashen biyu.”
Har ila yau, kamfanin jirgin saman China Eastern Airlines na shirin kaddamar da wani jirgin da zai hada Shanghai da Delhi daga ranar 9 ga watan Nuwamba, yana aiki sau uku a mako.
Ma’aikatan jirgin a filin jirgin Kolkata sun yi bikin ta hanyar kunna fitulun mai na gargajiya, yayin da jami’an ofishin jakadancin kasar Sin suka bayyana ranar a matsayin “mai matukar muhimmanci ga dangantakar Indiya da Sin.”
BBC/Aisha. Yahaya, Lagos