Take a fresh look at your lifestyle.

Rikicin PDP Ya Kara Ta’azzara Yayin Da Anyanwu Ya Kori Shugaban Jam’iyyar Da Wasu

12

A martanin da ya mayar dangane da dakatarwar da aka yi masa, sakataren jam’iyyar PDP na kasa, Sanata Samuel Anyanwu, ya sanar da dakatar da shugaban jam’iyyar na kasa, Ambasada Umar Iliya Damagum, da wasu ‘yan kwamitin aiki na kasa (NWC) bisa zarge-zargen cin zarafin jam’iyyar.

A yayin zantawa da manema labarai a Abuja ranar Asabar da ta gabata Anyanwu ya ce matakin ya biyo bayan wani taron gaggawa da kwamitin shari’a da ladabtarwa na jam’iyyar NLDCA ya yi, wanda ya kira kamar yadda kundin tsarin mulkin PDP ya tanada.

A cewarsa, “A matsayina na sakataren jam’iyyar na kasa, wanda ke da hurumin kiran taro na jam’iyyar NWC, duk wani taron da ban kira ba ya zama banza.”

Ya ce taron gaggawar ya yi nazari kan hukuncin da kotu ta yanke na baya-bayan nan da kuma ayyukan wasu ‘yan kungiyar NWC inda aka yanke shawarar dakatar da Damagum na tsawon wata daya “saboda rashin iya aiki, almubazzaranci da kudaden jam’iyya, da rashin bin hukuncin kotu.

Anyanwu ya yi zargin cewa Damagum ya yi watsi da shawarwarin doka kuma ya ci gaba da rike wani jami’in da aka kora a hukumar ta NWC, wanda hakan ya bata tarurrukan da yanke hukuncin da suka saba wa kundin tsarin mulkin jam’iyyar da kuma hukuncin kotu.

Sauran wadanda aka dakatar na tsawon kwanaki 30 sun hada da Mataimakin Shugaban Jam’iyya  Na kasa (Kudu), Ambasada Taofeek Arapaja; Sakataren Yada Labarai na Kasa, Hon. Debo Ologunagba; Sakataren kudi na kasa; Shugaban matasan na kasa, Muhammad Kadede; da mataimakin sakataren kasa, Setonji Koshoedo.

Anyanwu ya zargi jami’an da tafka laifuka daban-daban da suka hada da rashin da’ar kudi, rubuta wasiku ba bisa ka’ida ba, da kuma rashin tattara sassan jam’iyyar yadda ya kamata. Ya ce duk jami’an da aka dakatar an mika su ga kwamitin ladabtarwa don ci gaba da bincike tare da yiwuwar korar su.

“Muna yabawa bangaren shari’a kan hukuncin da aka yanke a jiya, wanda hakan nasara ce ga daukacin ‘ya’yan PDP a fadin kasar nan,” inji shi. “Duk da haka, ba za mu iya yin watsi da ayyukan wasu mambobin NWC da suka haifar da rashin jituwa tare da ficewar wasu gwamnoninmu da masu ruwa da tsaki daga jam’iyyar.”

Ya nada Mataimakin Shugaban Arewa ta Tsakiya a matsayin Shugaban riko na kasa, da Daraktan Yada Labarai na Jam’iyyar, Chinwe Nnorom, a matsayin Sakataren Yada Labarai na riko. Da yake amsa tambayoyi kan halaccin matakin da ya dauka, Anyanwu ya dage cewa yana yin aiki ne cikin ikonsa.

“Duk wata sanarwa na duk wani taro na NWC dole ne sakataren kasa ya ba da shi kamar yadda ya tanada a sashe na 36 (1) (g-h) na kundin tsarin mulkin mu. Abin da suka yi a baya ya sabawa doka,” inji shi.

Ya kuma yi watsi da shawarwarin da ke nuna cewa rikicin waje ne ke haddasa rikicin, ko kuma rashin warware rikicin cikin gida, yana mai cewa, “Idan gwamnoninmu da shugabanninmu suna ficewa daga jam’iyyar, hakan ya nuna gazawar shugabanci, shi ya sa ya kamata mu dauki mataki yanzu don ceto PDP.

Wannan ci gaban dai ya nuna wani sabon salo ne a rikicin shugabancin da ya dabaibaye jam’iyyar adawa, bayan hukuncin da kotun ta yanke a ranar Juma’a da ta dakatar da shirye-shiryen babban taronta na kasa.

 

Aisha. Yahaya Lagos

 

Comments are closed.