Take a fresh look at your lifestyle.

An Rantsar Da Samia Hassan ‘Yar Tanzaniya A Matsayin Shugabar Kasa

14

An rantsar da shugabar kasar Tanzaniya Samia Suluhu Hassan a ranar Litinin da ta gabata a kan karagar mulki a wa’adin mulkinta na farko bayan da ta samu gagarumin rinjaye a zabe mai cike da takaddama wanda ya haifar da zanga-zanga a fadin kasar.

Hassan, wanda ya hau kan karagar mulki a shekarar 2021, bayan rasuwar magabacinta, an ayyana ta a matsayin wanda ya lashe zaben makon jiya da kashi 97.66 na kuri’un da aka kada.

Sanye da jajayen gyale da duhun gilashi, ta yi rantsuwar kama aiki a wani biki da aka yi a sansanin soji da ke Dodoma babban birnin kasar.

Hassan, mai shekaru 65, ta fafata ne da ‘yan takara daga kananan jam’iyyu ne kawai bayan da manyan masu kalubalantarta daga manyan jam’iyyun adawa biyu aka hana su takara.

Zanga-zangar ta barke ne a yayin zaben na ranar Larabar da ta gabata, inda wasu masu zanga-zangar suka kona gine-ginen gwamnati da kuma ‘yan sanda suka harba barkonon tsohuwa da harbe-harbe, a cewar shaidu.

 

Reuters/Aisha. Yahaya, Lagos

Comments are closed.