Majalisar Dattawa Ta Bukaci A Tallafawa Kanfanonin Sufurin Jiragen Sama na Cikin Gida
Abdulkarim Rabiu
Majalisar Dattawan Najeriya ta jaddada bukatar tallafawa da karfafa gwiwa ga kanfanin jiragen sama na cikin gida a Najeriya, a daidai lokacin da ake zargi da kuma rashin fahimta game da wani lamari da ya faru kwanan nan da ya shafi wani jirgin Air Peace a Port Harcourt, Jihar Rivers.
Shugaban Kwamitin Jiragen Sama na Majalisar Dattawa, Sanata Abdulfatai Buhari, ya yi wannan kiran a Abuja ranar Alhamis a wani zaman bincike na kwana daya kan bukatar karfafa tsaron jiragen sama a Najeriya.
Taron binciken ya biyo bayan rahoton farko na Hukumar Binciken Tsaron Najeriya (NSIB) kan lamarin da ya faru kwanan nan a filin jirgin sama na Kasa da Kasa na garin Fatakwal.
Sanata Buhari ya ce yawancin zarge-zargen da ke tattare da lamarin ba su da tushe kuma ya yaba wa kamfanonin jiragen sama na cikin gida, ciki har da United Airlines da Air Peace, saboda hadin gwiwarsu da jajircewarsu ga tsaro.
“Muna bukatar karfafa gwiwa da gode wa kamfanonin jiragen sama na cikin gida. Suna yin iya Kar kokarinsu, kuma suna gudanar da bincike kan matukan jirginsu da ma’aikatansu akai Kai kafin su bar su su tashi,” in ji shi.
Ya kuma bukaci kafafen yada labarai da su taimaka wajen gina kwarin gwiwa a masana’antar jiragen sama ta hanyar bayar da rahoton bayanai masu inganci da gaskiya.
Ya ce Majalisar Dattawa, a cikin wani kudiri na baya-bayan nan, ta ba da umarnin cewa dukkan hukumomin gwamnati, ciki har da sanatoci, su yi amfani da kamfanonin jiragen sama na gida don tafiye-tafiye a hukumance don tallafawa masana’antar.
A cewarsa, kwamitin zai gabatar da rahoton binciken ga Majalisar Dattawa a cikin makonni biyu zuwa uku masu zuwa.
Shugaban Kamfanin Air Peace, Mista Allen Onyema, ya ce jirgin da ake bincike ba shi da wata matsala, ya kara da cewa babu wata illa da ta faru a jirgin.
“Jirgin ya tashi ya koma Legas, ba shi da wata damuwa ko kadan. Abin da ya faru kuskure ne na ɗan adam, domin matukin jirgin da ake magana a kai ya shefe kusan shekaru 40 ya tukin jirhin sama.
“Shi matukin jirgi ne ƙwararrene; ya samu akasi ne a ranar . A wannan rana, bai saurari shawarar mataimakin matukin jirginsa ba, wanda ya ba shi shawara kan lokacin da zai sauka,” in ji shi.
Ya bayyana cewa ba zai so ya yi cikakken bayani game da abin da ya faru ba saboda rahoton NSIB har yanzu yana ci gaba, yana ba da shawarar cewa a yi taka-tsantsan yayin gudanar da binciken, idan aka yi la’akari da yanayin da fannin ke ciki.
Mista Onyema ya ce bai kamata zaman binciken Majalisar Dattawa ya mayar da hankali kan Air Peace kawai ba tunda yawan zirga-zirgar jiragen sama na faruwa a duk duniya a cikin kamfanonin jiragen sama daban-daban.
“Da farko ban so in amsa wannan gayyatar ba, amma, da tunani na biyu, na zo ne saboda membobin Majalisar Dattawa abokan cinikinmu ne, kuma suna da dukkan ‘yancin damuwa da tsaro.
“Duk da haka, dole ne in gyara wasu ra’ayoyi da taken ko batun da aka yi amfani da shi don wannan zaman ya haifar.
“Abin da muke faɗi a nan ana sa ido a kansa a duk duniya. Dole ne mu yi taka-tsantsan kada mu kawo cikas ga sahihancin rahoton NSIB ko kuma mu lalata amincewar jama’a ga kamfanonin jiragen saman Najeriya.
“Air Peac ya na ɗaya daga cikin kamfanonin jiragen sama mafi aminci a duniya, ba wai a Najeriya kaɗai ba,” in ji shi.
Tun da farko, a cikin jawabinta kan lamarin, Manajan Darakta na Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama ta Najeriya (FAAN), Mrs Olubunmi Kuku, ta ce an gwada jajircewar hukumar wajen kare lafiya a lokacin jirgin saman Air Peace ya zarce hanya bayan ya sauka.
A cewarta, tawagar agajin gaggawa ta yi kokarin mayar da martani mai kyau kan lamarin.
“Babu rahoton raunin da aka samu ga fasinjoji 96 da ma’aikatan jirgin bakwai.
“Haka kuma, an kwashe dukkan fasinjoji da ma’aikatan jirgin zuwa ginin tashar jirgin lafiya.
“An rufe titin jirgin na ɗan lokaci bisa ga ka’idojin tsaro, kuma an fara aiki da tsari, da kuma sake bibiyar tsarin kare lafiya a filin tashin jiraren saman,” in ji ta.
Abdulkarim Rabiu