Uwargidan Shugaban Najeriya Oluremi Tinubu ta ce idan mata suka samu karfin gwiwa zasu iya zama masu kawo sauyi ga iyalansu da kuma al’umma baki daya.
Ta bayyana hakan ne a ranar Alhamis din da ta gabata a wajen bikin rufe horaswar da aka yi na horas da kungiyar ta Renewed Hope Initiative, inda mata 300 da aka zaba daga sassan kasar suka ci gajiyar shirin.
Horon wanda aka shirya tare da haɗin gwiwar wani kamfanin fasaha mai zaman kansa wato HUAWEI ne ak yi wa mata lakabi da Shirin Koyar da Fasaha.
Ta bayyana cewa shirin wanda yayi daidai da ajandar sabunta bege(Renewed Hope Agenda) na Shugaba Bola Tinubu don inganta ci gaban da ya shafi inganta fasahar dijital ga dukkan ‘yan Najeriya zai kara habaka tattalin arziki ta hanyar samar da masana’antu da ƙididdiga.
“Wannan shirin horon ya dace da lokacin da yake da fa’ida mai nisa. Yana da ikon ƙarfafa fannin dijital wanda zai bawa Mata ‘yan kasuwa dabarun fasaha don haɓaka kasuwancin su kuma su shiga cikin ma’ana a cikin tattalin arzikin dijital, da kuma zama zakarar gwajin canji na dijital a cikin al’ummominsu. “in ji ta.
Misis Tinubu ta bukaci wadanda suka ci gajiyar shirin da su tabbatar sun cigaba da sabunta iliminsu domin fasahar zata cigaba da canzawa.
“Ga mahalarta kodayake horon ya ƙare fasaha na ci gaba da canzawa. Babban abun yi shine ci gaba da koyo, haɓakawa, da kuma daidaitawa ga sababbin abubuwan da ke samuwa don ci gaban ku a fasaha.
“Yi amfani da sabbin fasahohin ku don magance matsaloli na gaske a cikin al’ummominku daban-daban, saboda kirkire-kirkire na gaskiya yana da amfani ne kawai idan ya inganta rayuwa. Ku tuna cewa kuna cikin babbar hanyar sadarwa sabida haka ku tallafawa juna kuma ku girma tare,” in ji ta.
Misis Tinubu ta ba su tabbacin cewa gwamnati zata ci gaba da yin duk mai yiwuwa don biyan buƙatun fasaha da tattalin arziƙin al’ummarta fiye da miliyan 250 musamman tare da taimakon ƙungiyoyin kamfanoni masu kyakkyawar manufa irin su Huawei.