Najeriya Ta Fara Tattaunawar Diflomasiyya Da Amurka Kan Ikirarin Da Ta Yi Kanta Kwanan Nan
Abdulkarim Rabiu
Najeriya ta bude hanyoyin sadarwa na diflomasiyya da Washington don tunkarar batun ayyana ƙasar a matsayin “Wadda za a Sanyawa ido ” da Amurka ta yi kwanan nan, bayan kalamai da barazanar da Shugaba Donald Trump ya yi.
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da kan Jama’a, Mohammed Idris, ya bayyana hakan a ranar Alhamis yayin da yake yi wa manema labarai jawabi a Fadar Shugaban Ƙasa bayan taron Majalisar Zartarwa ta Tarayya wanda Shugaba Bola Tinubu ya jagoranta.
Ministan ya jaddada cewa “kisan ɗan Najeriya ɗaya ya kasance babban abin damuwa ga Gwamnatin Najeriya, ya sake nanata cewa Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ya ba wa kowane ɗan ƙasa ‘yancin yin addininsa ba tare da wata tsangwama ba.
Idris ya ce; “Ayyana Najeriya a matsayin ƙasar da Amurka za ta sanyawa ido . Hakika, hakan ya taso ne a lokacin tattaunawa a taron Majalisar Zartarwa ta Tarayya, amma mafi mahimmancin abin da nake so in faɗi shi ne cewa gwamnatin Najeriya tana mayar da martani ga ainihin damuwar da aka taso.
“A bar batun siyasa, da gaske muna ɗaukar batutuwan da muhimmanci, amma bari in ce gwamnati, ko da kafin waɗannan abubuwan da suka faru a ‘yan kwanakin nan, ta himmatu sosai wajen tabbatar da cewa Najeriya tana da aminci ga kowa.”
“Kisan ko da ɗan Najeriya ɗaya yana damun gwamnatin Najeriya, kuma ba shakka, saboda kundin tsarin mulkinmu, kuma muna ci gaba da ambaton wannan, yana tabbatar da ‘yancin kowa na bauta wa addininsa ba tare da wani cikas ba. Gwamnatin Najeriya ta himmatu ga hakan, za ta ci gaba da yin hakan, kuma duk inda aka sami wani tashin hankali da ya shafi kowane ɗan ƙasa a wannan ƙasar, gwamnatin Najeriya tana da alhakin tabbatar da an magance shi,” in ji shi.
Idris ya sake nanata alƙawarin gwamnati na kare haƙƙin kundin tsarin mulki na kowane ɗan ƙasa na rayuwa da bauta cikin ‘yanci, yana mai alƙawarin cewa za a ci gaba da ɗaukar matakai masu tsauri kan duk wani tashin hankali don kare rayuka da tsaron dukkan ‘yan Najeriya.
Ya ce; “Wannan ba rfashin daukar batun da mahinmanci ba. shin akwai matsalolin tsaro a wannan ƙasar? Eh, akwai. Shin ana kashe mutane a sassan wannan ƙasar? Eh. Amma akwai wani abu da gwamnati ke yi – akwai wani abun da gwamnati ke yi don tunkarar matsalar? Haka ne, akwai. Shin gwamnati ma tana mayar da martani ga wannan? Haka ne. Amma ana yin hakan ne da babban nauyin da ke kanmu yayin da muke kiyaye daidaiton da muke buƙata don fuskantar waɗannan batutuwa kai tsaye.
“Yanzu, bari in sake nanatawa, eh, gwamnati tana mayar da martani ga wasu daga cikin waɗannan batutuwa ta hanyar da za ta nuna ko mu wanene a matsayinmu na ƙasa, tana kiyaye girmamawa da mutuncinmu a matsayinmu na ƙasa, da kuma maraba da haɗin gwiwar da muke buƙata daga kowa, da al’umomin duniya, don magance wannan batu.”
“Batutuwan ta’addanci, tashin hankali daga masu tsattsauran ra’ayi, ba abu ne da a ke yi a ƙasa ɗaya ba.
“Muna da iyakoki masu zurfi kuma shi ya sa muke haɗin gwiwa da abokan hulɗarmu na yanki. Muna kuma da haɗin gwiwa da abokan hulɗa na ƙasashen duniya, gami da Amurka da Najeriya za su ci gaba da hulɗa. Yanzu, shin mun yi wata tattaunawa da gwamnatin Amurka? Haka ne. An buɗe hanyoyin sadarwa. Mun fi son a magance wannan lamari ta hanyar diflomasiyya,” in ji Idris.
Ministan Yaɗa Labarai ya ƙara da cewa Gwamnatin Najeriya ba ta cikin wani yanayi na firgici amma tana mayar da martani cikin natsuwa, da kuma muradun ƙasa.
Ya sake nanata cewa Najeriya za ta ci gaba da kasancewa ƙasa mai juriya ga addini kuma tana ci gaba da hulɗa da abokan hulɗa na cikin gida da na ƙasashen waje don magance duk wata damuwa da ta shafi haƙƙin ɗan adam da tsaronta.
Idris ya ce; “Ba ma son ƙara zuguiguita maganganun da kuka faɗa, mun riga mu faɗa hakan. Nauyin da rataya akan mu a matsayinmu na gwamnati shi ne mu tabbatar kare lafiyar yan kasarmu a kan duk wata damuwa, gwamnatin Najeriya za ta ci gaba da yin hakan.”
“Amma babu wani yanayi na firgici a nan. Muna mayar da martani cikin nutsuwa, a hankali, kuma don muradun ƙasarmu, muna kuma la’akari da damuwar da ke cikin da wajen ƙasar nan game da abin da ke faruwa. Amma bari in nanatawa, Najeriya ƙasa ce da ke da jutiya ga addini,” in ji Ministan.