Take a fresh look at your lifestyle.

Shugaba Tinubu Ya Sha Alwashin Kawar da Ta’addanci

Abdulkarim Rabiu,

22

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa Najeriya za ta kawar da ta’addanci cikin nasara, yana mai tabbatar wa ‘yan kasa cewa gwamnatinsa tana kara karfafa hurdar diflomasiyya da kasashen duniya da kuma hanzarta kokarin dawo da zaman lafiya da tsaro mai dorewa a fadin kasar.

Shugaban ya yi wannan sanarwar ne a zauren majalisar da ke fadar shugaban kasa, Abuja, jim kadan kafin ya jagoranci taron Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) da kuma rantsar da sabbin Ministoci biyu domin shiga majalisar ministocinsa.

A wani martani da ya mayar kan ayyana Najeriya a matsayin ’’kasar da Amurka za ta Sanya wa ido’’ da kuma barazanar da shugaban Amurka Donald Trump ya yi na yiwuwar daukar matakin soji a karkashin fakewar kare ‘yancin addini, Shugaba Tinubu ya tabbatar da cewa “gwamnatinsa tana hada kai da al’ummar duniya ta hanyar diflomasiyya yayin da take ci gaba da jajircewa wajen kawar da ta’addanci da kuma tabbatar da zaman lafiya a kasa.”

Ya ce; “Abu mafi mahimmanci shi ne cewa duk da matsalar siyasa da fargabar mutanenmu za su ci gaba da tattaunawa da abokan huldarmu.

“Don haka aikin da ke gabanmu yana da girma. Muna tattaunawa da kasashen duniya ta hanyar diflomasiyya, kuma muna tabbatar muku da cewa za mu yi nasara akan ta’addanci a kasar.”

“Aikin da ke gabanmu yana da girma amma mun kuduri aniyar ci gaba da hadin kai da manufa, bisa tanadin kudirin sabunta fata wato (Renewed Hope), ajandar gina Najeriya mai wadata, hadin kai da jajircewa. Na gode kwarai da gaske,” in ji Shugaba Tinubu.

 

Abdulkarim Rabiu

Comments are closed.