Kotun kolin kasar Guinea ta tabbatar da cewa shugaban mulkin sojan kasar Mamady Doumbouya tare da wasu ‘yan takara takwas za su iya shiga zaben shugaban kasar da za a yi a wata mai zuwa.
Lokacin da Doumbouya ya karbi ragamar mulkin kasar Afirka ta Yamma a shekarar 2021, ya yi alkawarin ba zai nemi mukami ba.
Sai dai wani sabon kundin tsarin mulkin da aka kafa, wanda gwamnatin da sojoji ke jagoranta suka amince da shi a zaben raba gardama da aka gudanar a watan Satumba, yanzu ya share fagen neman takararsa.
Wasu manyan ’yan takara biyu, wadanda suka hada da tsohon shugaban kasar Alpha Conde da tsohon Firaminista Cellou Dalein Diallo, sun samu rashin cancantar su saboda shekaru da kuma ka’idojin zama da aka sanya a cikin sabon kundin tsarin mulkin kasar.
Doumbouya ya gabatar da sunansa a makon da ya gabata, matakin da ka iya ci gaba da rike shi na tsawon shekaru biyar. Yana takara a matsayin mai zaman kansa
Zai fafata da ‘yan takara masu karamin karfi kamar Abdoulaye Yero Balde, tsohon ministan ilimi kuma mataimakin gwamnan babban bankin kasa, da Faya Millimono, Dan adawa mai sukar gwamnatin mulkin soja.
Lansana Kouyate, tsohon Firayim Minista da ba a amince da takararsa ba, yana shirin daukaka kara, in ji jam’iyyarsa. Gwamnatin Doumbouya a shekarar 2022 ta ba da shawarar mika mulki na shekaru biyu zuwa zabe bayan tattaunawa da kungiyar ECOWAS ta yankin, amma ta kasa cika wannan wa’adin.
Zaben da aka shirya gudanarwa a ranar 28 ga watan Disamba na da nufin kawo sauyi a hukumance zuwa mulkin farar hula.
Reuters/Aisha. Yahaya, Lagos