Take a fresh look at your lifestyle.

Gwamnatin Najeriya Ta Bukaci A Kwantar Da Hankali Kan Takaddamar Diflomasiyya Da Amurka

208

Gwamnatin tarayya ta bukaci ‘yan Najeriya da su yi hakuri su kwantar da hankalinsu bisa la’akari da al’amuran diflomasiyya da ke tsakanin Najeriya da Amurka.

A wata ziyarar ban girma da ya kai wa gwamnan Jihar Jigawa Umar Namadi, ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa, Mohammed Idris, ya jaddada muhimmancin al’amarin a Dutse, Jihar Jigawa.

“Shugaba Bola Ahmed Tinubu yana da duk abin da ake bukata don tabbatar da Najeriya daga abubuwan da za su tada zaune tsaye, tare da gyara duk wata matsala da ke tsakanin kasarmu da abokanmu da abokan huldar mu na duniya. Don haka ya kamata ‘yan Najeriya su kwantar da hankalinsu,” in ji Idris.

Ministan yada labarai ya je Jihar Jigawa ne domin halartar taron gangamin matasa na yankin Arewa maso Yamma 2025 da kuma gabatar da nasarorin da shugaba Tinubu ya samu bayan shafe shekaru biyu yana mulki.

 

Aisha.Yahaya, Lagos

Comments are closed.