Shugabar kasar Tanzaniya Samia Suluhu Hassan ta sanar da gudanar da bincike a hukumance kan tarzomar da ta barke a makon zabe, biyo bayan zargin gwamnatinta da murkushe zanga-zangar mai cike da tarihi.
Tare da kwamitin binciken, shugaba Samia ta bukaci masu gabatar da kara da su yi sassauci ga mutanen da aka kama dangane da tashin hankalin.
Kalaman nata na zuwa ne kwanaki kadan bayan da babban jami’in kare hakkin bil’adama na MDD, Volker Türk, ya bukaci hukumomin kasar Tanzaniya da su gudanar da cikakken bincike na gaskiya kan rahotannin kashe-kashe da sauran munanan laifukan take hakin bil’adama a lokacin da kuma bayan zaben na ranar 29 ga watan Oktoba.
A yayin wani jawabi da ya yi wa majalisar a ranar Juma’a da ta gabata
shugaba Samia ta bukaci masu gabatar da kara da su yi la’akari da rage ko kuma janye tuhumar da ake yi wa mutanen da tashe-tashen hankula ba su da cikakkiyar fahimta game da ayyukansu.
“Ina sane da cewa an kama matasa da dama ana tuhumar su da laifin cin amanar kasa, ba su fahimci abin da suke shiga ba.
“A matsayina na uwa kuma mai kula da wannan kasa, ina umurtar hukumomin tabbatar da doka, musamman ofishin DPP, da su nuna sassauci.”
Samia ta kuma yi kira ga jam’iyyun siyasa da su hadu su tattauna yadda za a gudanar da siyasa ba tare da kawo illa ga kasa ba. Ta jaddada kudirinta na fara sabon tsarin samar da kundin tsarin mulki.
BBC/Aisha. Yahaya, Lagos