Minista Matawalle Ya Yi Allah-Wadai Da Harin Da Aka Kai Makarantar Kebbi Inda Ya Ba Da Umarnin Ceto.
Karamin Ministan Tsaro, Dakta Bello Mohammed Matawalle, ya yi Allah-wadai da mummunan harin da aka kai da daddare a makarantar ‘yan mata ta gwamnati da ke garin Maga, Jihar Kebbi, inda ya ba da umarnin daukar matakin gaggawa da hadin gwiwa domin ganin an sako daliban da aka sace.
Lamarin ya faru ne a Masarautar Zuru ta Danko karamar hukumar Wasagu inda ya yi sanadin kashe mataimakin shugaban makarantar Malam Hassan Yakubu Makuku tare da sace dalibai.
Ministan ya bayyana harin a matsayin abin da ba za a amince da shi ba, ya kuma umurci hukumomin tsaro da su yi aiki tare bisa umarnin Shugaba Bola Tinubu.
A cewar wata sanarwa da ma’aikatar ta fitar, Ministan ya jaddada cewa gwamnati ta bayar da umarnin gudanar da ayyukan tsaro cikin gaggawa domin ganowa tare da kwato daliban da aka sace.
Ya yi kira ga mazauna al’ummomin da abin ya shafa da su kwantar da hankula yayin da gwamnati da jami’an tsaro za su shawo kan lamarin.
Ya kuma jajantawa iyalan marigayi mataimakin shugaban makarantar da dukkan iyalan wadanda harin ya shafa, yana mai addu’ar Allah ya jikansa da rahama.
Ministan ya jaddada kudirin gwamnati na gurfanar da masu laifin a gaban kuliya da kuma karfafa tsaro a kusa da makarantu a cikin al’ummomin da ba su da karfi a fadin kasar nan.
Aisha. Yahaya, Lagos