Gwamnatin Jihar Nasarawa ta sake gargadin jama’a kan yada labaran karya ko kuma wadanda ba’a tantance ba wadanda za su iya kawo cikas ga zaman lafiya da ake samu a jihar.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban sakataren yada labaran gwamnan Ibrahim Adra kuma aka rabawa manema labarai.
Adra ya bayyana cewa gargadin ya zama dole ne biyo bayan wani rahoton karya gaba daya da aka yi na sace dalibai a karamar hukumar Doma.
A cewarsa sakamakon binciken da hukumomin yankin da shugaban makarantar da kuma sauran jama’ar yankin suka tabbatar da cewa ba a samu irin wannan lamari ba.
Rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa ta bakin jami’in hulda da jama’a ita ma ta fitar da sanarwar karyata rahoton.
Ya bukaci ‘yan kasar da su yi watsi da wannan gargadi na karya su kuma kasance masu bin doka da oda yana mai ba su tabbacin cewa gwamnati na nan a jajirce wajen ganin ta kare rayuka da dukiyoyi a fadin jihar.