Take a fresh look at your lifestyle.

Mataimakin Shugaban Kasa Zai Wakilci Shugaba Tinubu A Taron AU-EU

50

Bayan kammala ganawarsa a taron koli karo na 20 na shugabannin kasashen G20 a Afirka ta Kudu, mataimakin shugaban kasar Kashim Shettima ya tashi daga birnin Johannesburg zuwa Luanda domin wakiltar shugaba Bola Tinubu a taron kolin kungiyar AU da EU da aka shirya gudanarwa a Angola.

Mataimakin shugaban kasar zai bi sahun sauran shugabannin kasashen kungiyar tarayyar Afirka AU da kungiyar tarayyar Turai EU domin halartar taro karo na 7 na bangarorin biyu, wanda aka shirya gudanarwa daga ranar 24 zuwa 25 ga watan Nuwamban shekarar 2025 a babban birnin kasar Angola, Luanda.

Taron na AU da na EU zai hada shugabannin matasa, masu kirkire-kirkire da kuma kungiyoyin farar hula don yin tunani kan wasu kalubalen da kungiyoyin biyu ke fuskanta.

Har ila yau, za ta ba da shawarwari kan yadda za a magance matsalolin da suka shafi sauyin yanayi, haɗa kai a cikin ci gaba, samar da ababen more rayuwa, tattalin arziƙin dijital, masana’antar kere kere, masana’antu, da kasuwancin noma.

Mataimakin shugaban kasar zai dawo gida Najeriya a karshen taron kungiyar AU da EU.

Aisha. Yahaya, Lagos

Comments are closed.