Take a fresh look at your lifestyle.

Shugaban Najeriya Ya Ba Da Umarnin Janye Jami’an ‘Yan Sanda Daga VIP

67

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin janye jami’an ‘yan sandan da a halin yanzu ke samar da tsaro ga Muhimman Mutane VIPS, a kasar.

An bayar da umarnin shugaban kasa ne a taron tsaro da shugaba Tinubu ya gudanar a ranar Lahadin da ta gabata tare da ‘yan sanda, sojojin sama, hafsoshin soji da kuma babban daraktan hukumar tsaro ta farin kaya, DSS, a Abuja.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar, Mista Bayo Onanuga ya fitar, shugaban ya ba da umarnin cewa “daga yanzu, hukumomin ‘yan sanda za su tura karin rundunar domin mai da hankali kan ayyukansu na ‘yan sanda.”

A cewar umarnin shugaban kasa, “VIPs da ke son kariya daga ‘yan sanda, yanzu za su nemi ma’aikatan da ke dauke da makamai daga Hukumar Tsaro da Tsaron Farar Hula ta Najeriya.

Sanarwar ta ce; “Yawancin sassan Najeriya, musamman lungu da sako, ba su da ‘yan sanda kadan a tashoshin, wanda hakan ya sa aikin kariya da kare jama’a ya zama mai wahala.

“Bisa la’akari da kalubalen tsaro da kasar ke fuskanta a halin yanzu, Shugaba Tinubu yana da burin bunkasa ‘yan sanda a dukkan al’ummomi.”

Tuni dai shugaba Tinubu ya amince da daukar karin jami’an ‘yan sanda 30,000.

Har ila yau, gwamnatin Najeriyar na hada kai da jahohin kasar domin inganta cibiyoyin horar da ‘yan sanda a fadin kasar.

Taron na ranar Lahadi ya samu halartar babban hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Waidi Shaibu; babban hafsan sojin sama, Air Marshal Sunday Kelvin Aneke; babban sufeton ‘yan sanda, Kayode Egbetokun; da Darakta-Janar na Ma’aikatar Ayyuka ta Jiha, Tosin Adeola Ajayi.

 

Aisha. Yahaya,  Lagos

Comments are closed.