Take a fresh look at your lifestyle.

Biodun Oyebanji Ya Yi Rantsuwar Kama Aiki Na Mukamin Gwamnan Ekiti

0 268

Mista Biodun Oyebanji ya yi rantsuwar kama aiki a matsayin gwamnan jihar Ekiti a yankin Kudu maso yammacin Najeriya.

 

An rantsar da shi ne ta hannun babban alkalin jihar Ekiti, Hon. Mai shari’a Oyewole Adeyeye a ranar Lahadi 16 ga watan Oktoba.

 

Babban Alkalin Jihar Ekiti kuma ya rantsar da mataimakiyar Gwamna Oyebanji, Cif (Mrs) Monisade Afuye. Ta yi rantsuwar ne a daidai karfe 12:46 na rana.

 

Manyan mutanen da suka halarci taron sun hada da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu; Gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu da takwaransa na jihar Filato, Simon Lalong.

Sauran sun hada da Gwamna Babajide Sanwo-Olu (Lagos), Godwin Obaseki (Edo), Abubakar Badaru (Jigawa), Dapo Abiodun (Ogun), Atiku Bagudu (Kebbi) da dai sauransu.

 

Biodun Oyebanji ya tsaya takarar gwamnan jihar ne a ranar 18 ga watan Yuni, a karkashin jam’iyyar APC, ya samu kuri’u 187,057 inda ya doke babban abokin hamayyarsa, Segun Oni na jam’iyyar Social Democratic Party, wanda ya samu kuri’u 82,211 da Otunba Bisi Kolawole na jam’iyyar Peoples Democratic Party. wanda ya samu kuri’u 67,457.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *