Take a fresh look at your lifestyle.

Guinea-Bissau Sun Kada Kuri’a Ya Yin Da Shugaban Ke Neman Wa’adi Na Biyu

41

Kasar Guinea-Bissau mai fama da juyin mulki ta kada kuri’a a ranar Lahadin da ta gabata a zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokoki, inda shugaba Umaro Sissoco Embalo ke fafatawa don zama shugaba na farko cikin shekaru 30 da suka gabata da ya sake lashe wa’adi na biyu a jere a kasar dake yammacin Afirka.

Yana fafatawa ne da wasu ‘yan takara 11, wanda mafi karfi daga cikinsu shi ne Dan takarar siyasa Fernando Dias, wanda ke samun goyon bayan jam’iyyar da ta jagoranci yakin neman ‘yancin kai daga Portugal a shekarun 1960 da 1970.

An hana waccan jam’iyyar, wato African Party for Independence of Guinea da Cape Verde, gabatar da ‘yan takararta a karon farko bayan da hukumomi suka ce ta gabatar da takarda a makare.

Manazarta na hasashen Sun ce za a fafata tsakanin Embalo da Dias, kuma za a gudanar da zagaye na biyu na zaben idan babu Dan takara da ya samu sama da kashi 50% na kuri’un da aka kada.

Sanye da jan keffiyeh na al’ada, Embalo ya kada kuri’a a ranar Lahadi a birnin Gabu da ke gabashin kasar, yana mai nuna kwarin gwiwar cewa zai yi nasara.

“Ina kira ga kowa da kowa ya kada kuri’a da yawa, don zaben mutumin da zai kawo kwanciyar hankali da ci gaba a Guinea-Bissau, don gina kasar,” in ji shi.

An fara kidayar kuri’u jim kadan bayan rufe rumfunan zabe da karfe 1700 agogon GMT.

Yawan kuri’un da aka kada ya zarce kashi 65% kuma za a sanar da sakamakon wucin gadi a ranar Alhamis, kamar yadda kakakin hukumar zaben kasar Idrissa Diallo, ya shaida wa manema labarai da yammacin jiya Lahadi.

 

Reuters/Aisha. Yahaya, Lagos

Comments are closed.