Take a fresh look at your lifestyle.

Shugaba Tinubu Ya Shiga Taron ECOWAS kan Guinea-Bissau

42

A ranar Alhamis ne shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya halarci wani babban taro na musamman na kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka (ECOWAS) da ta kira domin magance rikicin siyasa da ke kunno kai a kasar Guinea-Bissau.

 

Ya hadu da sauran shugabannin Afirka ta Yamma ta hanyar Zoom Shugaba Tinubu ya shiga tattaunawa mai zurfi da nufin tabbatar da zaman lafiya da kuma tabbatar da tsarin mulkin kasa sakamakon abubuwan da suka faru a kasar.

 

Taron wanda aka gudanar a ranar 27 ga watan Nuwamban 2025 ya zo ne a daidai lokacin da ake kara nuna damuwa kan tashe-tashen hankula na siyasa da rashin tabbas na tsaro a kasar Guinea-Bissau.

 

A cikin wata sanarwa da kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Kimiebi Imomotimi Ebienfa ya sanyawa hannu gwamnatin Najeriyar ta bayyana matukar damuwarta dangane da juyin mulkin da sojoji suka yi a jamhuriyar Guinea-Bissau a baya-bayan nan tana mai bayyana hakan a matsayin sauyin gwamnati da ya sabawa kundin tsarin mulkin kasar wanda ke barazana ga ci gaban dimokuradiyya da zaman lafiyar yankin.

 

Sanarwar ta kuma yi Allah-wadai da matakin da sojojin suka dauka a matsayin wani mataki na karya ka’idojin dimokuradiyya da kyakkyawan shugabanci na kungiyar ECOWAS wadda ta haramtawa duk wani yunkuri na karbar mulki ta hanyar da ba ta dace ba.

Comments are closed.