Take a fresh look at your lifestyle.

Kifewar kwale-kwale Ya Kashe Mutane 20, Da Dama Sun Bata A Congo

259

Akalla mutane 20 ne aka tabbatar da mutuwarsu, yayin da wasu da dama suka bace, bayan da wani kwale-kwalen fasinja ya kife a tafkin Maï-Ndombe da ke arewa maso yammacin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo.

Mazauna yankin sun ce jirgin na kan hanyar zuwa Kinshasa ne a lokacin da lamarin ya faru a daren ranar Alhamis da ta gabata.

A cewar Diocese na Inongo, “sabon limamin Katolika da aka naɗa yana cikin fasinjojin da ke cikin jirgin.”

Wani mazaunin Inongo, Emmanuel Bola ya ce “kwale-kwalen ya taso ne daga Kiri kuma ya kife a tsakanin kayaking Bobeni da Lobeke da misalin karfe 8 na dare.”

Har yanzu dai gwamnatin Kongo ba ta fitar da adadin wadanda suka mutu a hukumance ba.

Gwamnan lardin Maï-Ndombe, Kevani Nkoso, ya shaidawa gidan talabijin na kasar cewa za a bayar da cikakkun bayanai bayan kungiyoyin agajin sun kammala tantancewar.

Hatsarin jiragen ruwa na yawaita a yankin, inda rashin kyawun hanyoyin sadarwa ke tilastawa mutane da yawa dogaro da tasoshin Jiragen katako wadanda galibi ke cika kaya kuma ba su da rigar ceto.

Da yawa kuma suna tafiya da dare, abin da ke sanya ayyukan ceto ke da wahala kuma ba a san inda aka kashe da dama ba.

A farkon wannan watan, wani hadarin kwale-kwale ya yi sanadin batan fasinjoji 64, yayin da sama da mutane 190 suka mutu a irin wannan bala’i a watan Satumba, wanda ake dangantawa da rashin yin lodi da kuma zirga-zirgar dare.

 

Labaran Afirka /Aisha. Yahaya, Lagos

Comments are closed.