Rundunar ‘yan sandan kasar Tunisia ta cafke fitacciyar ‘yar adawa Chaima Issa a wani zanga-zanga a babban birnin kasar Tunis domin aiwatar da hukuncin daurin shekaru 20 a gidan yari, in ji lauyoyinta.
Wata kotun daukaka kara ta yanke hukuncin daurin shekaru 45 ga shugabannin ‘yan adawa da shugabannin ‘yan kasuwa da kuma lauyoyi a ranar Juma’a da ta gabata, bisa zargin hada baki da hambarar da shugaba Kais Saied, a cikin abin da masu suka ce “alama ce ta kara samun karfin mulki.”
A yayin zanga-zangar, gabanin kama Issa, ita da biyu daga cikin wasu ‘yan siyasa da aka yanke wa hukunci sun yi kira ga gungun ‘yan adawa da su hada kai tare da kara yin zanga-zangar adawa da Saied.
Yace; “Za su kama ni nan ba da jimawa ba, ina gaya wa jama’a, ku ci gaba da zanga-zangar kuma ku yi watsi da zalunci, muna sadaukar da ‘yancinmu a gare ku.”
Ta bayyana tuhumar a matsayin rashin adalci da siyasa.
Ana sa ran ƙarin kame
Ana kuma kyautata zaton ‘yan sanda za su kame Najib Chebbi, shugaban jam’iyyar adawa ta National Salvation Front, babbar jam’iyyar kawance da ke kalubalantar Saied.
“Ba za mu sami ‘yanci ba sai da hadin kai,” in ji Chebbi, wanda aka yanke masa hukuncin shekaru 12 a gidan yari, a wurin taron.
“Muna shirye don zuwa gidan yari, ba ma jin tsoro,” in ji wani Dan adawa Ayachi Hammami, wanda aka yanke masa hukuncin shekaru biyar.
Yace; “Ina fatan matasa za su fadada zanga-zangar har sai hukumomi sun sake duba, ko kuma a shafe su da son jama’a.”
Saied ya ce yana yaki da maciya amana, masu cin hanci da rashawa da kuma ‘yan amshin shata.
Yana zargin kungiyoyin fararen hula da karbar kudade daga kasashen waje da nufin yin katsalandan a harkokin kasar Tunisiya.
An tuhumi mutane arba’in a shari’ar, daya daga cikin manyan laifukan siyasa a tarihin Tunisiya.
An tuhumi mutane arba’in a shari’ar, daya daga cikin manyan laifukan siyasa a tarihin Tunisiya.
20 daga cikin wadanda ake tuhumar sun tsere zuwa kasar waje kuma an yanke musu hukunci.
Hukuncin dai ya kasance daga shekaru biyar zuwa 45, kamar yadda wata takardar kotu ta nuna.
Kungiyoyin kare hakkin bil adama sun ce hukuncin wani yunkuri ne na murkushe masu adawa da Saied tun bayan da ya kwace ikoki na musamman a shekarar 2021.
Human Rights Watch da Amnesty International sun yi kira da a soke hukuncin nan take.
An daure masu suka, ’yan jarida da masu fafutuka, sannan an dakatar da kungiyoyi masu zaman kansu.
Reuters/Aisha. Yahaya, Lagos