Shugabancin jam’iyyar Labour na kasa Sun ,a kaddamar da wani kwamitin rikon kwarya mai mambobi 24 na jihar Ebonyi a wani mataki na maido da kwanciyar hankali da mayar da jam’iyyar matsayi domin gudanar da harkokin siyasa a nan gaba.
An gudanar da bikin kaddamarwar ne a karkashin ikon shugaban jam’iyyar na kasa, Sanata Nenadi Usman, da sakataren kasa, Sanata Darlington Nwokocha. Gogaggen dan siyasa, Cif Henry Udeh, wanda aka fi sani da Ajim Best wanda aka nada shi shugaban kwamitin riko, mai wakiltar Ebonyi ta Kudu.
An nada Comrade Innocent Igiri daga Ebonyi ta tsakiya a matsayin Sakatare, yayin da Mista Joshua Igwebuike daga Ebonyi ta Arewa aka nada Sakataren
Tsare-Tsare.
Haka kuma an nada Hajiya Rabiu Abubakar daga Ebonyi ta Arewa shugabar mata ta jiha domin inganta hada jinsi a cikin jam’iyyar.
A cewar jam’iyyar, “Hajia Abubakar za ta yi aiki kafada da kafada da shugabannin mata na shiyyar, da suka hada da Cif Misis Ngozi Nwaleke (Ebonyi North), Misis Ngozi Ekuma (Ebonyi South), da Blessing Okoroafor (Ebonyi Central), domin inganta shigar da mata a fadin jam’iyyar.”
Don ci gaba da karfafa tsarin ayyukanta a jihar, jam’iyyar Labour ta kuma nada Ike Nwobo a matsayin mai baiwa jihar shawara kan harkokin shari’a da Comrade Louis Nwebonyi a matsayin sakataren yada labarai.
Ana sa ran kaddamarwar zai kawo karshen rashin tabbas na tsawon watanni da aka kwashe ana fama da matsalolin cikin gida da suka shafi harkokin jam’iyyar a jihar Ebonyi.
Da yake mayar da martani ga ci gaban, shugaban jam’iyyar kuma Dan takarar gwamna a jihar a 2023, Kwamared Splendor Eze Oko, ya bayyana kwarin gwiwa ga shugabancin riko.
Oko ya ce, masu ruwa da tsaki da jiga-jigan jam’iyyar a shirye suke su yi aiki tare domin sake gina hadin kai da kuma karfafa tasirin jam’iyyar.
Hakazalika, Dan takarar majalisar wakilai na jam’iyyar Labour a 2023 mai wakiltar mazabar tarayya ta Abakaliki/Izzi, Mista Ezeh Emmanuel Ezeh, ya bayyana kaddamarwar a matsayin wanda ya dace.
Ya jaddada matsayin jam’iyyar a matsayin sahihanci da juriya na adawa a jihar Ebonyi.
Aisha. Yahaya, Lagos