Take a fresh look at your lifestyle.

Gwamna Yusuf Ya Yabawa Aikin Titin Kano

48

Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya yabawa Shugaban Kasa Bola Tinubu bisa amincewa da sa hannun gwamnatin tarayya wajen kammala aikin titin Wuju-Wuju da aka dade ana watsi da shi a Kano kan kudi naira biliyan 47

Yabon na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Sunusi Bature ya fitar. 

Gwamna Yusuf ya bayyana hakan ne a yayin taron Majalisar Zartaswa na Jihar karo na 35 inda ya bayyana aikin a matsayin wani muhimmin aiki na samar da ababen more rayuwa tare da fa’idar tattalin arziki da zamantakewa ga mazauna Kano. 

Ya tunatar da cewa an fara gudanar da aikin hanya mai mahimmanci tun a shekarar 2013 a lokacin gwamnatin tsohon Gwamna Sanata Rabi’u Kwankwaso amma ya samu tsawaita koma baya a tsawon shekaru wanda hakan ya sa aka yi watsi da shi.

A cewar Gwamnan, gwamnatin sa bayan ta tantance aikin ta nemi Gwamnatin Tarayya ta sa baki domin ganin an kammala shi.

Ya yi nuni da cewa bukatar ta samu kulawa cikin gaggawa inda har ta kai ga amincewar majalisar zartaswa ta tarayya zunzurutun kudi har biliyan ₦47 domin gudanar da ayyukan tituna masu dimbin yawa.

Gwamna Yusuf ya bayyana amincewar da Shugaba Tinubu ya samu a matsayin wata karara ta nuna kyakkyawan shugabanci da kuma jajircewa wajen samar da ababen more rayuwa musamman a jihar Kano. 

Gwamnan ya kuma baiwa shugaban kwamitin kasafin kudi na Majalisar Wakilai Hon. Abubakar Kabir Bichi bisa yabo ya yaba da jajircewarsa da bin diddiginsa daga Majalisar Dokoki ta kasa zuwa fadar shugaban kasa ta Villa wajen ganin aikin ya samu amincewar karshe. 

Yace Hon. Bichi ya tsaya tsayin daka tun daga matakin farko har zuwa amincewa daga karshe, tare da kare muradun jihar Kano a duk tsawon wannan aiki. 

Gwamna Yusuf ya bayyana dan majalisar a matsayin wanda ya cancanta a matsayin jakadan jihar Kano a Majalisar Dokoki ta Kasa ya kuma bukaci sauran ‘yan Majalisar Tarayya daga jihar da su yi koyi da kwazonsa da kishin kasa da wakilcin da ya dace, ba tare da la’akari da siyasa ba. 

Gwamnan ya kara da cewa Rawar da Hon. Bichi ke takawa wajen gudanar da wasu muhimman ayyukan gwamnatin tarayya na Kano da suka hada da Cibiyar Taro na kasa da kasa da ke kan titin Maiduguri da kuma filin wasa na kasa da kasa a Bichi. 

Ya yi amfani da damar wajen yin kira ga Shugaba Tinubu da ya amince da karin wasu manyan ayyukan more rayuwa ga Kano ganin matsayinta na daya daga cikin jihohin da ke da yawan al’umma a fadin kasar nan. 

Ya sake jaddada shirin gwamnatin sa na hada kai da Gwamnatin Tarayya don kara kaimi mai dorewa. 

Gwamna Yusuf ya tabbatar wa al’ummar Kano cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da bin dabarun hadin gwiwa da za su samar da ribar dimokuradiyya da dorewar ababen more rayuwa a fadin jihar.

 

Comments are closed.