Take a fresh look at your lifestyle.

Shugaba Tinubu Ya Gana Da Paul Kagame A Birnin Paris

48

Shugaba Bola Tinubu ya yi wata ganawar sirri da shugaban kasar Ruwanda Paul Kagame a birnin Paris na kasar Faransa, inda shugabannin biyu suka tattauna kan harkokin duniya da kuma batutuwan da suka shafi Afirka.

Bikin cin abincin da aka rufe shi ne karon farko da shugaba Tinubu zai bayyana a bainar jama’a tun bayan da ya bar Najeriya a ranar 28 ga watan Disamba, zuwa Turai a hutun karshen shekara da kuma tunkarar wani aiki a hukumance a Gabas ta Tsakiya.

A ranar Lahadi, 28 ga watan Disamba ne shugaba Tinubu ya bar Legas domin ci gaba da hutun karshen shekara kafin ya tafi ziyarar aiki kasar Hadaddiyar Daular Larabawa.

A wata sanarwa da mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar a baya, ya bayyana cewa, “Sheikh Mohamed bin Zayed Al Nahyan, shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa ya gayyaci shugaban domin halartar bugu na 2026 na Abu Dhabi Sustainability Week (ADSW 2026).”

Taron wanda aka shirya gudanarwa a farkon watan Janairu a Abu Dhabi, taro ne na shekara-shekara na tsawon mako guda wanda ya hada da shugabannin gwamnati, da ‘yan kasuwa, da kungiyoyin fararen hula, don tsara makomar samun ci gaba mai dorewa.

Tare da taken: “Nexus na gaba: All Systems Go,” ana sa ran bugu na 2026 na ADSW don haɗa kishi tare da aiki a cikin ƙirƙira, kuɗi, da mutane, yayin da ke nuna hanyoyin ci gaba na duniya da juriya.

Ana sa ran shugaba Tinubu zai dawo Najeriya bayan kammala taron

 

Aisha. Yahaya, Lagos

Comments are closed.