Fadar shugaban kasar Afirka ta Kudu ta matsa kaimi don tabbatar wa ‘yan Afirka ta Kudu cewa jami’an tsaro na sa ido kan duk wata barazana ga jama’a.
An bayar da wannan tabbacin ne bayan da ofishin jakadancin Amurka ya ba da sanarwar tsaro ga ‘yan kasarta a Afirka ta Kudu cewa ‘yan ta’adda na iya yin shirin kai wani hari kan manyan tarukan jama’a a Sandton da ke birnin Johannesburg.
A wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta fitar ta ce ta lura da sanarwar.
“Gwamnatin Afirka ta Kudu ta lura da sanarwar ta’addancin da ofishin jakadancin Amurka ya bayar a shafinta na intanet. Wannan wani bangare ne na daidaitattun sadarwar gwamnatin Amurka ga ‘yan kasarta.
Sanarwar ta ce “Hakki ne da ya rataya a wuyan jami’an tsaron Afirka ta Kudu su tabbatar da cewa dukkan mutanen da ke cikin kasarmu suna cikin koshin lafiya.”
Ya ce jami’an tsaro na sanya ido kan duk wata barazana ga ‘yan kasa da kasa baki daya.
“Ana ci gaba da tantance barazanar kuma ana aiwatar da su don tabbatar da amincin kowa. Sanarwar ta kara da cewa idan bukatar hakan ta taso, gwamnatin Afirka ta Kudu ce za ta fara sanar da jama’a game da duk wata barazana da za ta iya fuskanta.
BBC/CO
Leave a Reply