Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dawo Abuja bayan ya halarci taron koli na duniya da ya gudana a birnin Seoul na kasar Koriya ta Kudu.
Ya sauka ne a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe na shugaban kasa a safiyar Juma’a.
Shugaban ya samu tarbar shugaban ma’aikatan fadar sa Farfesa Ibrahim Gambari da ministan babban birnin tarayya Mohammed Bello da kuma shugabannin hukumomin tsaro.
Yayin da yake jawabi a taron, ya bayyana shirin Najeriya na zama cibiyar samar da alluran rigakafi.
Shugaba Buhari ya kuma shaida rattaba hannu kan wata yarjejeniya tsakanin Najeriya da Koriya ta Kudu kan gyaran matatun Kaduna da Warri.
Ya kuma gana da ‘yan Najeriya a Koriya ta Kudu inda ya shawarce su da su kasance jakadu nagari a kasar.
Leave a Reply