Shugaban Najeria Muhammadu Buhari ya mika sakon ta’aziyya ga shugaban kasar Yoon Suk-yeo, gwamnati da jama’ar kasar Koriya ta Kudu, da kuma ga iyalan wadanda wannan mummunan lamari ya rutsa da su a garin Itaewon da ke gundumar Seoul.
Shugaban ya mika sakon addu’a ga wadanda suka samu raunuka cikin gaggawa, da fatan su samu lafiya da kuma ta’aziyya ga dukkacin al’ummar kasar, yayin da suke alhinin mutuwar mutane sama da 150 wadanda galibinsu matasa ne da kuma mutanen da suka kai shekaru ashirin da haihuwa.
Shugaba Buhari ya tabbatar wa Yoon cewa Najeriya na goyon bayan al’ummar Koriya a wannan lokaci mai wahala.
Leave a Reply