Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ne ke jagorantar taron gaggawa na majalisar tsaron kasar a zauren majalisar da ke fadar shugaban kasa ta Villa, Abuja.
Wadanda suka halarci taron akwai mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha.
Sauran sun hada da ministocin tsaro, Manjo Janar Bashir Magashi, na harkokin ‘yan sanda, Maigari Dingyadi da kuma ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola.
Babban hafsan hafsoshin tsaro, Janar Lucky Irabor ya jagoranci hafsoshin tsaro zuwa taron.
Sufeto Janar na ‘yan sanda, Usman Alkali kuma yana halartar taron tare da shugabannin sauran hukumomin tsaro.
Ana sa ran taron zai dauki kwararan matakai kan rahotannin baya-bayan nan na barazana ga zaman lafiya a Abuja babban birnin kasar da sauran sassan kasar.
Leave a Reply