An ceto wani bakin haure kana ana fargabar wasu 50 sun nutse bayan wani jirgin ruwa ya nutse a tekun Bahar Rum, kamar yadda jami’ai suka bayyana.
Mutumin ya shafe sa’o’i 24 a cikin tekun kuma ya ce ya yi imanin duk sauran mutanen da ke cikin jirgin sun mutu, a cewar kungiyar wayar da kan jama’a ta Alarm Phone Group da ke kula da layin gaggawa na bakin haure.
Jirgin ruwan ya taho ne daga Tunisiya, in ji shi, wurin da bakin hauren ke yin kasadar balaguro na isa Turai.
Rundunar sojin Malta ta ce wani jirgin ruwan fatauci ne ya kubutar da mutumin kuma aka kawo shi Malta don jinya.
Su da Alarm Phone ba su bayyana lokacin da aka ceto mutumin ba.
Reuters/Aisha. Yahaya, Lagos