Mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ne ke jagorantar taron majalisar zartarwa ta tarayya da aka fara da karfe 10:00 na safe agogon Najeriya ranar Laraba a zauren majalisar da ke fadar shugaban kasa ta Villa, Abuja.
Farfesa Osinbajo ne ya jagoranci taron ne bayan babu shugaban kasa Muhammadu Buhari da ke kasar Ingila domin duba lafiyarsa.
Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha; da shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari ne ke halartar taron.
Ministocin da suka halarci taron sun hada da na masana’antu, kasuwanci da zuba jari, Niyi Adebayo; Cikin gida, Rauf Aregbesola; Wasanni da Ci gaban Matasa, Sunday Dare; Kimiyya da Fasaha, Adeleke Mamora; Ayyuka da Gidaje, Babatunde Fashola; da Noma da Raya Karkara, Mahmood Abubakar.
Karamar ministar masana’antu, kasuwanci da zuba jari, Mariam Katagum; da kuma karamin ministan lafiya, Ekumankama Joseph Nkama ma suna wajen taron.
Anyi Shiru na mintuna ga Amaechi
Kafin a fara taron, sakataren gwamnatin tarayya Mustapha ya sanar da majalisar ministocin kasar game da rasuwar ministan sufurin jiragen sama na farko na Najeriya, Cif Mbazulike Amaechi.
Ya kuma yi kira ga majalisar da ta yi shiru na minti daya domin girmama marigayi Amaechi, wanda ya rasu a ranar Talata, 1 ga watan Nuwamba, 2022, yana da shekaru 92 a duniya.
Leave a Reply