An yi kira ga mata da su rika amfani da kansu wajen tantance cutar sankarar nono da ta mahaifa domin tabbatar da gano cutar da wuri da kuma magance ta.
Wannan shi ne ra’ayoyin masu ruwa da tsaki a Kaduna a yayin taron wayar da kan jama’a game da cutar daji da aka gudanar a dandalin wasan polo na chukker polo and country, dake Maraban Jos, jihar Kaduna arewa maso yammacin Najeriya..
Wadanda abin ya shafa sun hada da uwargidan gwamnan jihar Neja Dr Amina Sani Bello, kwamishiniyar lafiya ta jihar Kaduna Dr. Amina Baloni, da wasu kwararrun likitoci daga asibitin koyarwa na Barau dikko da gidauniyar agaji ta Medic Aid, Dr Saannon Yates da Dr Fatima Danbatta da dai sauransu.
A zantawarta da manenma labarai bayan kammala taron, uwargidan Gwamna jihar Niger, Dr Amina Sani Bello ta ce “idan mace na duba kanta akalla sau daya a wata lokacin da ta ke al’alada ko bayan ta gama, hakan zai taimaka wajen gano cutar da wuri da Kuma daukar matakin da ya dace kafin abin ya ta’azzara.”
Mista Idowu Johnson daga First Bank ya ce jigon wayar da kan jama’a shi ne wayar da kan ‘yan Najeriya musamman mata kan yadda za su kare kai da gano cutar kansar nono, duba da cewa a Afirka ana fama da cutar kansar nono.
Wani rahoto da hukumar lafiya ta duniya WHO ta fitar a shekarar 2017 ya nuna cewa Najeriya ce ta 7 a duniya wadda ke da yawan masu fama da cutar daji.
Muhimman abubuwan da suka faru a wajen taron sun kunshi jawabai daga masuruwa da tsaki na wayar da kan al’umma da kuma nuna mata za su gwajin cutar da kansu.
Abdulkarim
Leave a Reply