Kwamishinan yada labarai, al’adu da al’amuran cikin gida, na jihar
Borno, Baba Kura Abba Jato, ya fadi hakan a lokacin da yake jawabi a
wajen taron karawa juna sani na kwanaki 2, mai taken ‘’Sanin hanyoyin
da Dan Jarida zai kare kansa daga rikice-rikice’’ wanda Kungiyar ‘Yan
Jarida ta (NUJ) ta Kasa reshen jihar Borno ta shirya, a garin
Maiduguri, bubban birnin jihar Borno.
Kwamishinan Baba Kura Abba Jato, ya lura cewar ‘’Akasarin labaran
da suke fitowa daga wasu sassan Kasarnnan labaraine na kanzon
Kuregene, kuma labaraine wadanda suke tayar da husuma a kasa ta yadda
rikicin Kabilancin Kabila, ko Bangaranci, Siyasa da na Addini ke
tasiri, kuma wannan duk ya samo asaline a watsa labaran karya a
wadannan kafafe, to adon haka nike kira ga ku ‘Yan Jarida ku lalubo
wadansu hanyoyi wanda zai rika karyata wadannan kafafe ta yadda za’a
sami dawawwamammen zaman lafiya a Kasa.’’
A kasidar da ya gabatar mai taken ‘’Canza Tsarin aikin Jarida da
shi kanshi Dan Jarida,’’ Shehin Malami mai Koyar da aikin Jarida a
Tsangayar koyon aikin Jarida ta Jami’ar Maiduguri, Farfesa Danjuma
Gambo, ya ce’’ A yanzu lokaci ya yi da ‘Yan Jarida zasu sauya akalan
labaransu daga rubuta labarun kashe- kashe, ya zuwa labaun zaman
lafiya da ci gaban tattalin arziki, ganin cewar a yanzu haka an sami
cikakken zaman lafiya da walwala a daukacin jihar Borno dama wannan
Yanki na Arewa maso gabashi, sa’annan gwamntin jihar Borno ta dukufa
ka’in da na’in wajen gudanar da ayyukan raya Kasa.’’
Tun da farko sai da Shugaban Kungiyar ‘Yan Jarida ta Kasa reshen
jihar Borno, Malam Dauda Iliya, ya ce’’Kungiyar ta NUJ a jihar, ta
shirya wannan taron karawa juna sanine, saboda kokarin fahimtarwa tare
da wayar da kan mambobinta a dangane da sauke nauyin da ya kamata su
sauke na fadakarwa, gami da ilimantar da alumman jihar a dangane da
abin da ya shafi zamantakewa a tsakanisu.’’
Ya ce’’Kungiyar har ila yau a karkashin jagorancinmu, ta kuduri
aniyar kyautata rayuwa gami da jin Dadin mambobinta a ko da wani
lokaci, fadakarwa tare da tunasar da mambbobi ta fuskar gudanar da
ayyuka a duk in da suka samu kawunansu, ta yadda zasu sami saukin
gudanar da ayyuka.’’
Malam Yakubu Musa wakilin Kamfanin Dillacin Labarune ta NAN, na
daya daga cikin wadanda suka halarci taron karawa juna ilimin, ya fada
cewar’’Wannan taron karawa juna ilimi wanda Kungiyar NUJ ta Borno ta
shirya abune wanda ya zo dai-dai a kan gaba domin kuwa babu ko shakka
na karu kwarai da gaske ta fuskar gudanar da ayyukana, tare kuma da
yadda zan kare kaina a yayin da na samu kaina a cikin wani kangi,
domin masana sun gabatar da kasidu daban-daban tare da kawo misalai na
yadda zamu iya gudanar da ayyukanmu a ko da wani lokaci.’’in jishi.
Leave a Reply