Take a fresh look at your lifestyle.

CCB Ta Samar Da Tsarin Tattara Bayanan Kadarorin Ma’aikata

Abdulkarim Rabiu, Abuja

0 217

Shugaban hukumar dake kula da Daar Ma’aikata wato Code of Conduct Bureau CCB, Muhammad Isa ya bayyana cewa hukumarsa ta samar da wani tsari na tattara bayanai a yanar gizo wanda ko wane ma’aikacin gwamnatin zai cika bayyanan kaddarorin da ya mallaka.

Muhammad Isa ya bayyana haka ne a lokacin da Hukumarsa ta bayyana a gaban kwamitin Majalisar Wakilai akan yaki da cin hanci da rashawa domin kare kasafin kudin hukumar na shekara ta 2023 a Abuja.

Shugaban yace an samar da sabon tsarin tattara bayanan kadatrorin ta amfani da yanar gizo ne domin samun sauki wurin cika bayyanan kaddarorin Ma’aikata ya Kuma Kara da cewa an samar da yanayin da zai tabbatar da kyakkyawan tsaron takardu da bayyanan sirri na Ma’aikata.

Har ila yau shugaban ya ce an fara gwajin tsarin a jihohi goma sha biyar a fadin kasar nan Kuma duk ma’aikacin da aka gano cewa yana kashe kudaden da suka wuce abin da yake samu za a neme shi domin ya yi bayani akan inda ya samo su.

Daga bisani shugaban yayi kira ga kwamitin da ya taimaka wurin ganin yadda zaa karawa hukumar kudi a kasafin kudin shekara ta 2023 domin aiwatar da wasu muhimman ayyuka, bugu da Kari shugaban ya jaddada aniyar hukumar sa na ci gaba da wayar da kan al’umma akan manufofin hukumar.

A nasa jawabin shugaban kwamitin Hon. Shehu Garba tare da wasu membobin kwamitinsa sun tabbatar da cewa za su yi duk mai yiyuwa domin tallafawa Hukumomin gwamnati wajen tafiyar da aikinsu Kamar yadda ya kamata.

Sauran Hukumomin da suka bayyana a gaban kwamitin sun hada da Hukumar ICPC da kotun tabbatar da Daar Ma’aikata wato code of conduct tribunal

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *