Take a fresh look at your lifestyle.

Yan Wasan Neja Sun Kammala Shiri Na Zuwa Gasar Wassannin Motsa Jiki Na Kasa A Delta

Nura Muhammed, Niger state.

0 194

Ganin yadda wasanni motsa jiki na kasa ke Kara karatowa yanzu haka gwamnati jahar Neja Dake arewa ta tsakiyar Najeriya ta shiryawa Yan wasanta da zasu wakilci jahar a gasar wasanni motsa jiki da za a yi a jahar Delta inda zasu shiga sansanin horaswa domin Kara shirya su don ganin sun taka rawar a zo a gani a wasanni daban daban da zasu a fafata akai

Daraktan wasanni na ma’aikatar wasanni da ci gaban matasa na jahar Neja Alhaji Baba Sheshi shi ne ya bayana hakan a lokacin da yake ganawa da masu horaswa da Kuma sakatarorin kungiyoyi wasanni daban daban da za su shiga gasar Karo na 21.

Alhaji Baba Sheshi ya ce “sannanin horaswa na mako guda da yan wasan za su shiga ya sami amincewar kwamishinan wasanni da ci gaban matasa na Jahar Malam Yusuf Sulaiman”.

Daraktan ya ce
“Yan wasan da suka shiga sansanin za su rika karbar Naira dubu biyu a kowace rana a matsayin alawus na daukar horo na tsawon mako guda da zasu yi, sannan Kuma masu horas da su su karbi Naira dubu uku a kullum a matsayin suma nasu alawus”
Har ila yau ya ce ma’aikatar wasanni da ci gaba matasa ta jahar Neja ta samar da kayayyakin da suka dace ga Yan wasan don daukan Horan da Kuma motocin da za su rika jigilar su zuwa filayen wasanni.

Alhaji Baba Sheshi ya ce yanzu haka yan wasa 96 ne zasu shiga a fafata da su a gasar, sannan ya bukaci masu horas da su da sakatarorin kungiyoyin wasannin da su kara karfafawa yan wasan guiwa don ganin sun daga martabar jahar Neja a gasar wasannin motsa jikin.

Wannan dai wani yunkuri ne daga bangaran gwamnatin jahar Neja na ganin ta karfafawa matasa da za su wakilci jahar a wasannin motsa jiki na kasa a jahar Delta kudu maso kudanci Najeriya da za a fara daga ranar 28 ga wannan watan na Nuwamba zuwa goma ga watan December na wannan shekarar da muke cikin.

AK

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *