An nada Mrs Christy Uba a matsayin mai kula da masu yiwa kasa hidima, NYSC a Najeriya.
Sanarwar da Daraktan Yada Labarai da Hulda da Jama’a na shirin Mista Eddy Megwa ya fitar, ta ce tsohon Darakta Janar na NYSC, Birgediya Janar Muhammad Fadah ya mika ragamar shugabancin hukumar ga Mrs Uba a matsayin babbar Darakta a shirin. .
“Mrs Uba ta karbi ragamar jagorancin Corps a matsayin mai kulawa, har zuwa lokacin da Mista President zai nada babban Darakta.”
An nada Misis Uba bayan korar Birgediya Janar Fadah da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi a makon jiya.
Leave a Reply