Take a fresh look at your lifestyle.

An gudanar da addu’o’i na musamman a jihar Katsina

KAMILU LAWAL

0 215

Gwamnatin jihar Katsina ta shirya wani taro domin gudanar da addu’o’i na musamman da nufin samun zaman lafiya a jihar

 

 

Taron addu’o’in wanda ya gudana a masallacin juma’a na Usmanu Danfodio dake birnin Katsina ya ssmu halartar gwamnan jihar Aminu Bello Masari da yan tawagarsa da malamai daga bangarori da dama domin gudanar da addu’o’in da nufin neman dauki wajen Allah ya kawo karshen aiyukan ta’addanci da jihar ke fuskanta.

 

 

 

Jim kadan bayan gudanar da addu’o’in gwamnan Masari ya shaidama yan jarida cewa gwamnati zata cigaba da shirya addu’o’in ta la’akari da mahimmancin ta, yana mai godema Allah madaukakin Sarki bisa yadda jihar take samun zaman lafiya sannu a hankali tare da rokon maido da dawwamamnen zaman lafiya a jihar

 

 

 

Kazalika gwamnan ya yaba da irin hadin kan da ake samu a tsakanin kungiyoyin addinin Islama musamman ma a tarukkan addinai

 

 

 

Shima mai baiwa gwamnan shawara na musamman akan sha’anin tsaro Alhaji Ibrahim Katsina ya bukaci al’ummar jihar da su cigaba da gudanar da addu’o’in neman zaman lafiya a jihar da kasa baki daya

 

 

 

Ibrahim Katsina wanda ofishin sa ne ya shirya taron ya bayyana cewa an shirya taron addu’o’in ne domin samun zaman lafiya da hadin kai a tsakanin al’ummar jihar

 

 

 

Mai bawa gwamnan shawarar ya bayyana addu’a a matsayin hanyar magance kowane irin kalubale, yayi fatan addu’ar zata magance kalubalen tsaron da jihar ke fuskanta tare da maido da zaman lafiya a fadin jihar da kasa baki daya

 

 

 

A sakon sa da ya aiko, mai martaba sarkin Katsina AbdulMumini Kabir Usman ya jaddada bukatar hadin Kai a tsakanin al’ummar musulmi  domin cigaban al’umma

 

 

 

A lokacin taron addu’o’in dai an gudanar da karatun Alqur’ani mai girma da addu’o’i hadi da neman gafarar Allah madaukakin sarki domin samun zaman lafiya a jihar da kasa baki daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *