Ministan matasa da wasanni na Najeriya Sunday Dare, ya bi sahun gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa, domin karbar Fitilar Hadin kai ta Torch of Unity, wanda ke nuni da fara taron wasannin motsa jiki na kasa (NSF) karo na 21 a babban birnin jihar Asaba.
Shima babban sakataren ma’aikatar Ismaila Abubakar, ya bi sahun ministan wasanni da gwamnan jihar domin karbar Toch of Unity, bayan ya zagaya jihohi 36 na tarayya ciki har da babban birnin tarayya Abuja.
Torch of Unity na kasa karo na 21 ya fara motsi bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da shi a ranar Talata, 25 ga Oktoba, 2022 a fadar Aso Rock Villa, Abuja.
- Kara karantawa: NSF: Kimanin ‘Yan Wasa 14,000 Don Gasar Cin Kofin Lambobi
Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya wakilci Shugaban Kasa a wajen bikin ya bayyana cewa bikin wasanni dakin injin ne da ya samar da manyan zakarun wasanni na Najeriya wadanda suka rubuta sunan kasar da zinare.
Yayin da aka shirya gudanar da bikin bude taron a filin wasa na Stephen Keshi, dake Asaba a ranar Laraba, kasar na shirin ganin an samu karin hazaka da za su daga tutar kasar a matakin duniya.
Leave a Reply