Take a fresh look at your lifestyle.

Majalisar Wakilai Ta Amince Da Kudirin Kafa Jami’ar Kimiyyar Lafiya Da Fasaha A Kankia

Abdulkarim Rabiu, Abuja

0 2,004

Majalisar Wakilan Najeriya ta amince da kudirin kafa Jami’ar Kimiyyar lafiya da Fasaha ta Tarayya a garin Kankia, Jihar Katsina dake arewa maso yammacin Najeriya wadda Hon Abubakar Yahaya Kusada ya dauki nauyi.

Shugaban masu rinjaye a majalisar Alhassan Ado Doguwa shi ne ya gabatar da bukatar karatu na uku a kan kudirin dokar kuma ya zarta karatu na ukun.

Da yake tsokaci game da kudirin dokar ta kafa Jami’ar Kimiyyar lafiya da fasaha ta tarayya a garin Kankia-. wanda ya dauki nauyi kuma danmajalisa mai wakiltar mazabar Kankia/Kusada/Ingawa a majalisar tarayya, hon Abubakar Yahaya Kusada, ya bayyana cewa idan aka kafa jami’ar za ta kasance irinta ta farko a duk yankin Arewa maso Yammacin Najeriya.

Dan majalisar wanda kuma shi ne Shugaban Kwamitin Majalisar Mai kula da raba daidan ayyukan Gwamnatin Tarayya, ya ce Jami’ar za ta kasance da manufa daya na karfafa ci gaban koyo da koyarwa a fannonin kimiyya da fasaha na kiwon lafiya, da cibiyoyin bincike da cibiyoyi masu alaka da kimiyya da fasaha na kiwon lafiya.

Hon Kusada ya kara da cewa jami’ar za ta kuma ba da damar samun guraben shiga jami’o’i da daukar ma’aikata duk bisa ka’idojin da hukumar kula da jami’o’in Najeriya ta gindaya.

Yanzu haka dai za a mika kudirin ga Majalisar Dattawa domin samun daidaito ra’ayin a game da kudirin dokar.

Ga Abdulkarim Rabiu dauke da cikakken rahoto:

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *