Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranci taron majalisar zartarwa ta tarayya, wanda aka gudanar a dakin taro na fadar shugaban kasa dake Abuja.
Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari da shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya, Dr Folashade Yemi-Esan na daga cikin wadanda suka halarci taron.
Sauran sun hada da ministocin yada labarai, Lai Mohammed, kudi, kasafin kudi da tsare-tsare na kasa, Zainab Ahmed da Justice Abubakar Malami da dai sauransu.
Kafin fara shawarwarin ranar, shugaban ya kaddamar da wata takarda mai suna ‘Eyemark’, don sa ido da tantance manyan ayyukan gwamnati.
Majalisar ta kuma yi shiru na minti daya domin karrama tsohon ministan harkokin cikin gida da tsaro na Najeriya, Ademola, Rasaq Seriki, wanda ya rasu a ranar Alhamis 15 ga watan Disamba yana da shekaru 63 a duniya.
Har ya zuwa rasuwarsa, Marigayi Seriki ya kasance jakadan Najeriya a kasar Spain kuma wakilin kasar na dindindin a hukumar yawon bude ido ta duniya.
Leave a Reply